Gine-Ginen Da Akafi Kashe Ma Makudan Kudi A Fadin Duniya

Ginin majalisar dokokin kasar Romania, ginin ne da yafi kowannen gini tsada a kasashen turawa, littafin tarihi na duniya ya misalta wannan gini a matsayin gini da yafi kowanne tsada a duniya, an kiyasta kudin ginin da ya kai dallar Amurka billiyan $3.38B. Sabon ginin kasuwancin duniya shine gini da yafi kowane gini a duniya tsada “One World Trade Center” dake garin New York an kiyasta kudin ginin da ya kai dallar Amurka billiyan $3.9B.

Ginin Goldman Sachs, a garin New York, banki da yake da kusan komai a cikin shi don ma’aikata, ya hada da wajen wasanni da shakatawa duk a cikin ginin, an kiyasta kudin ginin da ya kai dallar Amurka billiyan $2.1B. Sai ginin The Shard, na kasar Ingila, yana daya daga cikin ginanuwan da su kafi tsawo a yankin kasashen turai, an kiyasta kudin ginin da ya kai dallar Amurka billiyan $2.18B.

Haka ginin Emirates Palace Hotel, a kasar Abu Dhabi, wanda yaci kudi da suka kai billiyan $3B. Wannan otel din yana daga cikin otel da sukafi kowannen otel tsada wajen gini a duniya. Yanada wajen saukan jirgi mai saukar angulu don baki da basu tafiya a mota.