Visa Wasu Kasashe 10 Da Su Kafi Wahala A Duniya

Babu wani mahaluki da ke son kyaluwa, kyama, ko kuma nuna halin ko oho ga mutun. Dukkan mutun nada bukatar a girmama shi a harkokin yau da kullun na duniya. Idan mutun mai sha’awar tafiye-tafiye ne kodai don kasuwanci ko yawon bude ido. To mutun ya sama ranshi cewar komai na iya faruwa da shi wajen neman izinin "visa" ta shiga wasu kasashe guda 10 da aka lissafo a matsayin kasashe da ke da wahalar samun damar shiga kasar ga baki.

Kasar China, itace ta farko a kasashe da ke da wahalar samun izinin shigan baki, idan mutun nada bukatar zuwa kasar, don hutu ko kasuwanci, wanda zai bukaci kwanaki sama da 30, ko kuma mutun zai ziyarci yankin kudanci kasar. To sai mutun ya nuna shedar otel, tikitin jirgi na komawa kasar su, da abun da zai kaishi kana da yawan kwanakin da zaiyi, duk dai wannan kan dauki mutun tsawon wata biyu zuwa uku.

Kasa ta biyu kasar Iran, tana daga cikin kasashe da suke tsaurara matakai wajen neman izinin shiga kasar. Mutun zai nemi izinin shiga ta hanyar ma’aikatar kulla da harkokin kasashen waje. Haka idan mace zata nema izini sai ta saka hoto da zai rufe mata jiki kamin su bata damar shiga kasar.

Kasa ta uku kuwa itace kasar Russia, tun bayan kaddamar da tsarin daukar hoton tafin hannu mutun, hakan yasa abun nasu yayi tsauri matuka. Ko kamun mutun ya nema izinin shiga kasar sai mutun ya samu takarda daga wasu hukumomi daga cikin kasar cewar suna gayyatar mutun, kana mutun zai hada takar dun shi ya aikia embasi na kasar a kasar su.

Kasa ta hudu kuwa itace kasar Turkmenistan, itace kasar da tafi kowace kasa boyon al’ammurran su na yau da kullun a tsakanin su da wasu kasashe, mafi akasarin hurdar su da sauran kasashen duniya ba kasafai suke zama a bude ba.

Kasa ta biyar kuwa Azerbaijan, itace kasar da tafi kowace kasa a duniya yawan hutu a hukumance, domin kuwa suna tafiya hutu na sati daya a lokaci daya. Suma idan mutun na neman izinin shiga kasar sai yayi rubuce rubuce da dama.