Yadda Zaben Nijar Ke Tafiya a Kano

'Yan Nijer Mazauna Najeriya

Wasu daga cikin masu jefa kuri’a sun koka kan yadda suka ce an tauye masu hakkin sun a jefa kuri’a saboda basu da katin zabe

Kimanin ‘yan Nijar mazauna Kano 700, ne ke jefa kuri’a domin zaben shugaban Kasa da ‘yan majalisar dokoki na kasar a karamin ofishin jakadancin Nijar dake Kano.

Da karfe takwas na safiyar lahadi ne aka bude runfunan zabe dake harabar karamar ofishin jakadancin jamhuriyar Nijar, dake Kano, Muhammadu Tasiu daya daga cikin Malaman zaben yace idan mutun yazo da katin zaben shi za’a duba idan aka sunan shi a bashi takardan jefa kuri’a da zaran an tantance mai jefa kuri’a shike nan.

Ya kara da cewa duk wanda baida katin zabe kuma babu sunan shi a kundin zabe toh atakaice bazai samu jefa kuri’a ba.

Koda yake wannan shine karo na biyu da hukomomin jamhuriyar Nijar suka baiwa ‘yan kasar dake kasashen waje damar jefa kuri’a amma ‘yan siyasa sun ce akwai gyara.

Wasu daga cikin masu jefa kuri’a sun koka kan yadda suka ce an tauye masu hakkin sun a jefa kuri’a saboda basu da katin zabe amma suna da wata katardan sheda mai nuna cewa sun ‘yan kasa ne.

Babban jami’in zabe ta CENI a babban cibiyar zabe ta Kano Alhaji Iliyasu Samaila yace wadanda suke da korafe basu da ainihin takardar shedar jefa kuri’a.

Your browser doesn’t support HTML5

Yadda Zaben Nijar Ke Tafiya a Kano - 3'31"