Shafin zumunta na facebook, ya kaddamar da wata dama ga masu amfani da wayoyin Android. Yanzu dai duk wayar da ke amfani da kimiyyar android, za’a iya bude account biyu a lokaci daya, musamman masu kokarin amfani da damar aika sakon gaggawa “messenger” mutane kan iya bude shafufuka biyu daga daya zuwa daya duk a kan waya daya.
Ana iya kara wani account a kan wayar batare da mutun na cikin shafin shi na facebook ba, kawai mutun kanyi amfani da shafin aika sakon gaggawan kadai, idan bukatar shiga shafin baki daya bata kama ba. Kuma ana iya amfani da wannan damar na messinja don yin bidiyo call wato mutun yaga mutun.
Idan kuwa har mutun nada damuwa dangane da wasu zasu iya shiga cikin account din shi don yi mishi binciken asiri, da zarar mutun ya zo shiga daya daga cikin account din, za’a bukaci ya saka sunan shi da kuma lambar sirri wanda shi kadai ya sani. Hakan ba zai bama wani damar shiga ba sai wanda yake da masaniya da ya dace.
Idan kuwa wani yayi kokarin yimaka kutse shafin facebook zasu aika maka da wani sako, da cewar ko kai ne kake kokarin shiga, wanda daga bisani idan ka amsa tambayoyin dai-dai sai abaka damar shiga kai tsaye.