Fiye da mutane 6000, ne aka yiwa rajista ‘yan asalin kasar Nijar domin jefa kuri’a a zaben da za’a gudanar a gobe idan Allah ya kaimu.
Shugaban ‘yan Nijar mazauna Najeriya, Abubakar Khalidou, ne ya furta haka ga wakilin muryar Amurka Nasiru Adamu Elhikaya a Abuja.
Yace za’a gudanar da zaben a Najeriya a wurare bakwai ne a Najeriya, Abuja, Lagos, Kano,Kaduna Sokoto Benin da Fatakwal, kuma kayayyaki zabe sun riga sun kai wadannan wurare in ji shugaban.
Ya kuma bukaci al’umar Nijar mazauna Najeriya, da kowa ya zabi wanda ya kwanta masa a rai, da kuma jan kunne cewa sun tabbatar da cewa an gudanar da wannan zabe cikin kwancyar hankali da luma na.
Yace idan fiti ta taso talaka zuwa masu dukiyar babu wani mai jin dadi, yana mai cewa siyasa ra’ayi ne kuma mutun daya ne zai lashe zabe saboda haka duk wanda Allah ya baiwa a taru a mara masa baya domin samu ci gaban kasar ta Nijar.
Your browser doesn’t support HTML5