Da dama mutane za suyi mamaki idan akace kasar Korea ta arewa “North Korea” itace kasa da tafi kowace kasa yawan cin hanci da rashawa a duniya. Kamar yadda wasu kasashe a nahiyar Afrika wutan lantarki tazama abun sha’awa gare su, to haka a kasar suma kashi 30% na mutane basu samun wutar lantarki. Hakan yasa kasar ta zamo ta daya a cikin jerin kasashe masu fama da cin hanci da rashawa.
Sai kasar Somalia, tun bayan juyin mulki a shekarar 1991, kasar ta shiga cikin halin kakani kayi wanda yasa wasu jami’an gwamnati ke wawusan arzikin kasar. Hakan yasa ta zamo ta biyu. kasar Afghanistan, ta zamo ta uku, wanda take da yawan mutane milliyan 32. Sai kasar Sudan, ita tazo ta hudu, kasar nada yawan mutane milliyan 38.4. Kasar Angola, ta zama ta biyar a cikin jerin kasashen, kasar nada yawan mutane sama da milliyan 25.1. Haka kasar Sudan ta kudu itama bayan rikice rikice ta shiga cikin wani yanayi na sace sace daga shugabanni, yawan mutane yakai milliyan 11.9 itace kasa ta shida. Sai kasar Iraq, da ke da yawan mutane sama da milliyan 35.2 ta zamo ta bakwai.
Kasar Libya, itace kasa ta takwas, wanda suke da yawan mutane milliyan 6.3. Haka kasar Haiti da ke kudu da kasar Amurka, tana da yawan mutane da suka kai milliyan 10.6 itace kasa ta tara. Kasa kuwa ta goma itace kasar Guinea-Bissau, suna da yawan mutane milliyan 1.8. Kasar Venezuela itace kasa ta goma sha daya cikin kasashe masu fama da cin hanci da rashawa a duniya. Kasar nada yawan mutane milliyan 30.9. Sai kasar Eritrea, da ke da yawan mutane milliyan 6.8, ta zamo ta goma sha biyu. Sai kasar Syria, ta zamo ta goma sha uku. Haka kasar Turkmenistan, kasar na da yawan mutane milliyan 5.9, itace kasa ta goma sha hudu. Ta goma sha biyar kuwa itace kasar Yemen, kasar nada yawan mutane milliyan 28.3.