An Fara Kidayar Jinsin Tsuntsaye Daga Ko'ina A Fadin Duniya

A wasu lokutta mutun ya kanji wasu abubuwa dake faruwa a fadin duniya, da ya kanyi mamaki wani lokaci kuma mutun ya kanga abun al’ajabi. A kasar India, cikin jihar Kashmir, yankin tsuburin “Himalayan wetlands” an fara gudanar da kidayar tsuntsaye. Tsuntsaye kanje yanki daga ko ina a fadin duniya, a kowace shekara.

Hakan ya jawo hankalin hukumomi da su dinga duba adadin yawan tsuntsayen dake zuwa yanki a kowace shekara, da kuma jinsin kowane irin tsuntsu, yanzu dai haka kimani sama da mutane 100 suke wannan yankin don fara wannan kididdigar da za’a kwashe kwanaki biyu a nayi.

An dai kwashe tsawon shekara daya ana wannan shirin don gudanar da wannan kidayar. A cewar wani jami’in aikin gandun daji Mr. Imtiyaz Lone, yace yanzu muna kidayar tsuntsayen ne ta hanyar kidayar kimiya ta zamani, da kuma sharudda da aka sa ta kasa-da-kasa wajen kare hakkin su tsuntsayen.

Domin kuwa a shekarar da ta gabata mun kidaya sama da tsuntsaye milliyoyi da dama. A tsuburai 13, amma a wannan shekarar muna sa ran kara yawan tsuburan zuwa 21. Ya kara da cewar, ga dukkan alamu bana baza’a samu yawan tsuntsaye ba kamar bara, saboda ire-iren canjin yanayi da ake samu a fadin duniya, hakan na shafar abubuwa da dama a duniya wanya ya hada da halittu da dama. Ana sa ran idan Allah ya kaimu watan gobe za’a bayyanar da sakamakon gidayatr tsuntsaye nawa suka halarci tsuburin.