Tsofaffin Shugabanin Amurka Da Abunda Suka Mallaka

Tsohon shugaban kasar Amurka George H. W. Bush, shine shugaban kasar Amurka na 15 da yafi sauran kudi, a cikin jerin sunayen tsofafin shugabannin kasar Amurka da yawan kudin su da kuma yadda suka samu kudin. Kamar yadda dan shi shima tsohon shugaban kasar Amurka George Bush, dukkan su sunyi aiki a matatun mai, wanda yasa yake da yawan kudi da suka kai dallar Amurka $23M milliyan.

Sai kuma shugaba John Quincy Adams, na 16 yana daga cikin tsofafin shugaban kasar Amurka da suka samu kansu cikin rudani da dama, wanda hakan yasa har ya rasa zaben shi a karo na biyu, shima dai ya gaji kudin shine a wajen mahaifin shi, kuma shima lauya ne. Yana da adadin dallar Amurka $21 milliyan. Haka shugaba George W. Bush shine na 17, wanda yake da yawan kudi da suka kai $20 milliyan, yanzu haka dai yana cigaba da samun kudi ta littafin da ya buga, da kuma zuwa wurare yana magana ana biyan shi.

Na goma sha takwas 18 kuwa shine John Adams, ya mallaki dallar Amurka $19M wanda yasamu matsala a zaben shin a karo na biyu da abokin hamayyar shi Thomas Jefferson ya kada shi. Shi kuwa na 19 shine Richard Nixon, ya mallaki kimanin dallar Amurka $15M duk dai da cewar ya samu matsala a wata badakalar Watergate da akayi a wancan lokacin. Tsohon shugaban kasar Amurka Ronald Reagan, shine shugaban kasa na 20 cikin jerin masu kudi, wanda ya mallaki kimanin dallar Amurka $13M kamin dai ya zamo shugaban kasar Amurka, an sanshi shahararen dan fina-finai ne a kungiyar ‘yan finafinai ta kasar Amurka Hollywood.