Wasu Jerin Garuruwa Da Sukafi Dadewa A Duniya

A kwai wasu garurwa a wasu kasashe a fadin duniya da sukafi dadewa kuma har ya zuwa yau suna nan kamar kullun, a wannan rahoton mun zakulo 20 da suka ga zamanoni da dama. Gari na farko shine Varanasi, na kasar india, garin dai yana dauke da dunbin tarihi, an kiyasta tsawon shekarun wannan garin da suka kai shekaru dubu fiyar 5,000.

Sai gari na biyu Cadiz, a kasar Spain wanda akwai mutane da suka zauna a garin tun shekara 1,100 da suka wuce kamin zuwan annabi Isah. Garin shima yana da dunbin tarhi inda jinsin Romawa suka zauna tun a karni na 18. Na uku kuwa shine garin Thebes, a kasar Greece, shi kuwa mutane da suka isa wannan garin a shekaru 1,400 da suka wuce kamin zuwan annabi Isah, yanzu dai garin ya zama kamar wata kasu. Gari na hudu kuwa shine Larnaca, a kasar Cyprus, shi dai garin mutane da dama daga wasu fadin duniya sukan ziyarci garin don gani ireiren ginananuwa da suke da shi, shima dai garin yana da shekaru 1,400 da suka wace.

Gari na biyar kuwa shine Athens, a kasar Greece, wannan garin na daya daga cikin garuruwa da aka yankema wayewa cibi, domin kuwa ya zama wata mahada ta jinsin mutane daban daban a fadin duniya, kuma an kiyasta shekarun garin sama da shekaru 7,000. Gari na shida kuwa shine Balkh, a kasar Afghanistan, shima dai gari ne da aka kiyas ta shekarun shi da suka haura 2,500 kamin zuwan annabi Isah.

Haka garin Kirkuk, a kasar Iraq, shine na bakwai, tun kimanin sama da shekaru 2,200 kamin zuwan annabi Isah mutane suka fara zama a wannan garin, har ya zuwa yau akwai ginanuwa da suka wuce shekaru 5,000 a garin, wanda yanzu haka shine babban birni da ke da arzikin mai a kasar ta Iraqi. Gari na takwas kuwa Arbil, duk a kasar Iraqi, shima yana da tsawon sama da shekaru 2,300. Na tara kuwa shine Tyre, a kasar Lebanon, da ke da tarihin mutane sun zauna a garin kimanin sama da shekaru 2,750 kamin zuwan annabi Isah.

Gari na 10 kuwa shine Jerusalem, a yankin kasashen larabawa, shi dai wannan garin yana da dunbin tarihi, a cikin garin ne babban masallacin Al-Aqsad yake, masallaci na uku a daraja, sai kuma Chocin Sepulcher, mutane sun fara zama a wannan garin tun a shekarar 2,800 da suka gabata kamin zuwan annabi Isah.