Ma'anar Bukin Ranar Masoya Nada Banbanci A Kowace Kasa

A duk ranar goma sha hudu 14, ga watan Fabrairu na kowace shekara, akan gudanar da bukin masoya a duniya. A kasar Amurka, wannan wata rana ce wadda take da dunbin tarihi, haka a wasu kasashen duniya sukan ware wannan ranar don gabatar da wasu bukukuwa na irin al’adun su. A kasar Japan, ‘yan mata kan shirya kyautar da zasu bama masoyan su wanda ya hada da yin Cakulet, suba masoyan su. Su kuma masoyan nasu sai su biya bashi a ranar 14 ga watan Maris, wanda ake gudanar da wani bukun na masoya.

Kasar Philippines, sukan ware wannan ranar ne domin ma’aurata su dinga tuna baya, da kuma yin wasu bukukuwa da zai kara tuna musu irin soyayar da suke ma juna. Mafi akasarin mutane akasar sukan yi bukin aure a ranar da ta fado ranar 14, don karfafa soyayya. Suma mutanen kasar Guatemala, sun dauki wannan ranar ne a matsayin ranar da mutane zasu hadu dangi da ma ‘yan-uwa da abokan arziki, don nuna farinciki da kauna ga juna. Gare su ba wai kawai saurayi da budurwa ko ma’aurata ne kawai zasu morema wannan ranar ba.

A kasar Africa ta Kudu kuwa, wannan wata ranace da samari zasu gane 'yanmatan da ke son su a boye. Domin kuwa a wannan ranar ne ‘yan mata zasu dauki kati mai dauke da alamar zuciya, wanda ke nuna alamar soyayya, sai su rubuta sunan wanda su keso, su kuma makala a inda kowa zai gani. Ta haka samari zasu gane wacece take son su, idan kuma tayi dai-dai da abun da yake so ne, sai su cigaba daga nan. A kasar Ghana, kuwa tun shekarar 2007, aka ware ranar 14 ga watan Fabrairu a matsayin ranar bukin Cakuleti a baki daya kasar. Taya kuma kuka gudanar da bukin masoyan ku a wannan shekar? Ku rubuto muna a shafin mu na dandalinvoafacebook.