Kadan Daga Cikin Jerin Garuruwa Da A Kafi Ziyarta A Duniya

A cigaba da kawo jerin garuruwa da su kafi samun baki a fadin duniya, garin New York a kasar Amurka, shine gari na 8, da yawan mutane milliyan 12.2, kana garin Istanbul na kasar Turkey, dake da milliyan 11.9, haka garin Kuala Lumpur, na kasar Malasia, da suka samun yawan mutane da suka kai milliyan 11.6, sai garin Antalya, a kasar Turkey, da suma suka samu mutane milliyan 11.5, haka suma garin Dubai a yankin daular larabawa da mutane a kowane lungu na duniya ke ziyarta, nada yawan mutane da suka kai milliyan 11.4 a shekara.

Haka garin Seoul a kasar South Korea, sun samu adadin mutane da suka kai kimanin mutane milliyan 9.4, sai babban birnin Rome, a kasar Italy da suka samu mutane milliyan 8.8, suma garin Taipei da yake babban birnin tarayya kasar Taiwan, sun samu mutane sama da milliyan 8.6, kana garin Guangzhou, a kasar China, sun kai kimanin mutane milliyan 8.2 a shekarar da ta gabata.

Suma garin Phuket, a kasar Thiland da suka samu kimanin mutane milliyan 8.1, haka suma garin Miani a jihar Florida da ke da babban wurin shakatawa da gane-gane a kasar Amurka, sun samu mutane da suka kai milliyan 7.3, garin Pattaya a kasar Thailand ba’a barsu a baya ba, domin kuwa sun samu mutane sama da milliyan 6.4, su kuwa garin Shanghai ta kasar China sune cikon gari na 20 da suka fi samun baki ‘yan ziyara a fadin duniya.