Daga wasan dusar kankara sai zuwa wasan tseren kan dusar kankara, kana da shan shayi mai dumi a lokacin sanyi a kasar Amurka. Wata hukuma mai lura da yanayin duniya, sun bayyanar da wasu garuruwa a kasar Amurka, a matsayin garuruwan da su kafi kowannen gari samun dusar kankara a tsawon kiman shekaru 30.
An dai fara wannan kididdigar ne, tun daga shekarar 1981 zuwa 2010, a tsakanin shekaru 30 an iya gano garuruwa 30 da su kafi samun matsananciyar dusar kankara. Gari na farko shine Niagara falls, a jihar New York, wanda a shekara suke samun dusar kankara da ta kai inci 76.1. Garin Dunkirk, shima duk a jihar ta New York, suna samun kimanin dusar kankara inci 79.1 a shekara, sai garin Oneonta, duk a jihar suna samun inci 79.1 na dusar kankara a shekara.
Kana da garin Wheat Ridge, da suke samun inci 81.0 a shekara, kana South Burlington, a jihar Vermont, suna samun inci 81.2 a shekara, sai garin Anchorage, a jihar Alaska, sukan samu kamar inci 82.1 a shekara. Haka suma garin Tooele, ta jihar Uta, sukan samu inci 83.0 na dusar kankara a kowace shekara. Garin North Tonawanda, a jihar New York, kan samu dusar kankara da ta kai kimanin inci 83.1 a shekara.