WASHINGTON DC, —
Daga shekarar 2007 zuwa yau Bashar Aliyu ya zana motoci kusan dari takwas (800) da wani abu. Abin da yaja ra'ayin Bashar wajen zanen motoci shine. Ya kasance yana sha'awar mota tun yana yaro, yakan ma yi motocin kwali na wasan yara tun yana karamin shi. Kuma tun yana kimanin dan shekaru 17, ya fara jin kwakwalwar shi zata iya kirkirar mota ya zana ta ajikin takarda.
An dai haifi Bashar Aliyu, ne a karamar hukumar Sakkwato ta Arewa, a cikin jihar Sakkwato, Bashar yayi karatun firamari a makarantar Mohammadu Zako Model Primary School, ya taba karatu a makarantar Gov't Tech College Runjin Sambo, daga baya ya koma makarantar Sultan Abubakar College, daga karshe dai ya samu kammala karatun sakandire a makarantar gwamnati da ke Dundaye.
A shekarar 2007 ne Bashar Aliyu ya fara zanen motoci, mota ta farko daya fara zanawa wadda ya sama suna "sky" da niyar zai kera ta tayi tafiya, amma daga baya ya fuskanci rashin kwarin gwiwa, wanda ya sanya bai samu damar yin wannan motar ba. Duk da hakan baiyi kasa a gwiwa ba sai ya ci gaba da zane-zanen shi na motoci.Bashar ya fara kirar kananan motoci kamar yadda aka nuna wadannan motocin da yake yi a kafafen watsa labarai, yana yin sune da wani kwali da ake kira Straw Bord, yana amfani da Top bond gam wurin hada wani bangare da wani.