Ina 'Yan-Makarantar Sakandiren Kasashen Afrika? Ga Damar Zuwa Amurka!

#6 Yale University

Daya daga cikin jami’o’in da sukayi fici a duniya, “YALE University” ta nan kasar Amurka, sun shirya wani taron karama juna sani, na yara matasa ‘yan makarantar sakandire da suka fito daga kasashen Afrika. Wannan horarswa kyauta ce batare da mutun ya biya kosisi ba, kuma za’a kawo matasan ne nan kasar Amurka don basu wannan horon.

An dai shirya wannan koyarwar ne ga matasa da suke kokarin kamala karatun su na sakandire, da zummar basu horaswa a fannoni daban-daban. Wannan horarwar ta shafi bangarori da dama, duk matashin da ya samu shiga wannan zababbu da zasu halarci koyarwar ta sati biyu, zasu samu damar koyon karatu daga malaman da sukayi fice a duniya.

A cikin jerin kwasa-kwasai da za’a koyar da matasan sun hada da fannin tsurar kimiyya da fasaha, (Applied Science & Engineering) a turance, da Ilimin dangantakar kasa-da-kasa tare da tsaro, (International Affairs & Security) a turance, kana da bangaren lafiya da hallittan dan’adam, (Biological & Biomedical Science) a turance, da Fasaha da kere-kere, da kasuwanci, haka kuma da bangaren ilimin makamashi da yanayi. (Technology, Innovation, & Entrepreneurship) a turance, Akwai bangaren siyasa, tattalin arziki, tare da karatun shari’a (Politics, Law, & Economics) a turance.

Ana bukatar duk wani matashi da ke da sha’awar yin karatu a waddannan bangarorin, da ya kokarta aika afilikeshan nashi da gaggawa. Wannan jami’ar zata dauki nauyin kudin jirgin yaro, da kuma abincin shi da otel nashi, na tsawon kwanakin da za suyi a nan kasar Amurka. Duk wanda ke da sha’awa sai ya kokarta kamin ranar 11 ga watan Fabrairu, 2016. Za kuma a samu wannan fom din shiga a shafin http://globalscholars.yale.edu haka kuma idan mutun na neman karin bayani ko wata tambaya sai a aika da sako zuwa wannan adireshin global.scholars@yale.edu Haka kuna iya rubuto muna tambayar ku kai tsaye a shafin mu na DandalinVOAfacebook