Na'urorin Zamani Kan Haifar Da Jidali Ga Al'umma

Da akwai bukatar lokutta da dama mutane suyi amfani da hankalin su wajen warware wasu matsaloli, musamman ma idan suka hada da abubuwan kimiyyar zamani, kamar su wayar hannu, kwamfuta, laptop, da dai makamantan su.

Wasu ma’aurata Christina Lee da mijinta Michael Saba, ita ‘yar jarida shi kuma Inginiya ne, suna da gidan su, a kusan kullun idan dare yayi sai mutane su buga musu da cewar network ya nuna musu cewar wayar su da aka sace tana gidan su. Mafi akasarin wayoyin zamani suna dauke da wani sinadari da zai iya bayyana ma mutun inda wayar shi take idan ta bace. Da dama idan mutane sun je gidan sai suyi musu bayani kan cewar su ba barayi bane, kuma basu siyan kayan sata, don haka basu da wata bakuwar waya a gidan su.

Abu dai yakai matuka sai suka sanar ma kamfanonin waya da cewar ana zuwa gidan su da suna neman waya, koda aka duba sai aka gano cewar wai idan gida na tsakanin karfen kamfanin waya, shike haddasa wannan sai ya nuna cewar waya tana duk gidan dake tsakanin falwayar biyu.

A takaice dai mutanen sun bukaci da kamfanonin su gyara wannan matsalar, don gujema wata matsala da hakan kan iya haifarwa, kusan da dama idan mutane sukaje gidan su, sai su gaya musu cewar wayar su bata gidan. A wasu lokkuta sukan rabu bacikin jin dadiba har ma wani lokaci sai an kira jami’an ‘yan-sanda. Don haka basu son abun da zai haddasa fitina, a lokacin da ake zantawa da matar da mijinta, sunce lallai idan mutun ya dinga dogara da wadannan naurorin suna iya kai shi ga akin danasani.