Kasuwar Da Tafi Yawan Shekaru Ana Kasuwanci Haryanzu A Ciki

Kasuwar Duniya

Kasar Turkey, itace kasa dake da kasuwar da tafi kowacce dadewa a duniya, wanda har ya zuwa yanzu kasuwar tana ci, tun a shekarar 1461 kimanin sama da shekaru 600 ke nan. Ita dai wannan kasuwa mai suna Grand Bazaar an fara gina tane a shekarun mulkin sarki Sultan Mehmet II, wanda daga baya kasuwar ta zama wata cibiyar cinikayyar duniya, mutane daga ko’ina a fadin duniya su kanje wannan kasuwar don saye da siyarwa, haka baki ‘yan yawon shakatawa sukan ziyarci wannan kasuwa.

A cikin wannan kasuwar akwai kimanin shaguna 4,000 haka kimanin sama da mutane 250,000 ke zuwa wannan kasuwar a kowace rana. Babu wani abun duniya da baza’a sameshi a wannan kasuwar ba, domin kuwa ta kunshi mutane na kowane irin jinsi a duniya. Hakan dai yasa kowa na son ziyartar wannan kasuwar idan damar hakan ta samu. Don tsarin wannan kasuwar kowane irin abun kake so akwai layin da zakabi don samun shi. Ita dai kasuwar tana da kofofi 21 na shiga da fita, kana da hanyoyin da suka hadu da juna 56. Haka kuma idan aka hada ta da sauran kasuwannin duniya, za’a ga cewar kayan cikin ta sunfi rahusa.

Uwa uba kasuwar tana hade da wani katafaren masallaci dake da wajen shakatawa da cin abinci harma da wasan yara duk a cikin shi.