A tarihin wasu garuruwa 3 a nan kasar Amurka sun samu dusar kankara da basu taba samu ba a duniya, garin Baltimore a jihar Marylan, sun samu dusar kankara da ta kai kimanin inci 29.2, sai garin Allentown a jihar Pennsylvania da suka samu dusar kankara inci 31.8 hakama babban birnin jihar Pennslyvania Harrisburgh sun samu kimanin inci 34, su kuma brnin New York sun samu inci 26.8.
Wannan dusar kankarar dai ta jawo abubuwa da dama, wanda kimanin sama da jirage 11,700 ne aka hana su tashi da sauka a jihohin yankin arewa maso gabas a nan kasar Amurka. Haka mutane da dama basu fita zuwa wajen aiki ba a ranakun Juma’a Asabar da Lahadi, wannan wani babban koma bayane ga tattalin arzikin kasar, domin kuwa mutane da dama sun shige cikin gida babu fita waje. Hakan dai yasa tsadar aikin gwadugo ya karu, domin kuwa a birnin New York ta kaiga ana neman mutane da zasu kwashe, dusar kankara a biyasu dallar Amurka $13.50 a duk awa, dai-dai naira 3,000 a duk awa mutun yayi yana kwasar dusar kankara.
A cewar shugaban karamar hukumar New York, mun samu dusar kankara da bamu taba samun irintaba, don haka dole dukkanmu mu tashi tsaye wajen ganin wannan bai haifar da rasa rayuka ba da dukiyoyin al’uma.