Najeriya, Ghana Da Kamaru Na Cogen Shekarun 'Yan-Wasan Su!

'Yan Kwallon U 17

A wani rahoto da wata hukumar kasa-da-kasa ta fitar da ke nuni da cewar, kasashen Najeriya, Ghana da Kamaru, na cikin kasashe da suke choge wajen bayyanar da shekarun gaskiya na ‘yan wasan su.

Ita dai hukuma da ke lura da yadda ake gudanar da wasana kwallo a duniya, ta kasar Switzerland, ta bayyanar da cewar har yanzu kasashen Afrika basu fahimci irin baiwar da Allah yayi musu ba, domin kuwa basu amfani da matasansu ta tsaftatatciyar hanya.

Sun kara da cewar duk dai da yadda kasashen su kayi a shekarar 2015 na saka ‘yan wasa masu kanana shekaru, kasashen 3 zasu cigaba da fuskantar matsaloli a filin daga.

An dai bayyanar da wannan rahoto ne a ranar 12 ga watan Janairu na wannan shekarar, inda aka ruwaito kasar Najeriya, Ghana, da C

KNamaru a matsayin kasashe da suka sanya ‘yan wasa da sukafi kowa kananan shekaru a cikin kasashe 50. A jerin shekaru da aka bayyanar a allon shekaru akwai ‘yan wasa masu shekaru 24.7 da 25.1 dama 25.3 a dukkannin yan wasan na kasashen 3.