Hukumomin Jamhuriyar Nijar su na ci gaba da tsare wasu manyan jam'iyyar MODEN Lumana da aka kama a karshen mako, yayin da aka hana su ganawa da lauyoyinsu.
Wakilin Sashen Hausa, Souley Moumouni Barma, yace wannan matakin yana shan suka daga kungiyoyi da 'yan rajin kare hakkin bil Adama.
Wakilin namu yace wadanda aka kama din sun hada har da dan majalisar kasa daga Tahoua, Ali Babati, da Seyni Mereda na reshen Yamai, sai Sani Bala na Maradi, da Oumarou Moumouni Dogari wanda aka kama a lokacin da yake shan mai a wani gidan mai na Yamai.
Haka kuma akwai Issoufou Issaka na Tilaberi wanda mai dakinsa Madame Hashiya Fatima ta ce har yanzu ba ta samu ganinsa ba.
Ta ce, "wasu jami'an farin kaya ne suka zo har gida suka yi awon gaba da maigidana. N abuga wayarsa ba ta shiga. Na je ofishin 'yan sandan farin kaya an ce ba ya nan. Naje dukkan wasu caji ofis na birnin Yamai, da ofishin yaki da ta'addanci, na kuma je ofishin 'yan sandan yaki da masu safarar miyagun kwayoyi, da kuma makarantar 'yan sanda. Duk inda naje an ce da ni ba ya nan."
Ta ce "ina fata za a sallami mai gidana ya dawo cikin iyalinsa."
Su ma lauyoyin wadannan 'yan siyasar sun ce an hana su ganawa da mjutanen da aka kama din, abinda ya fara harzuka wasu 'yan rajin kare hakkin bil Adama wadanda suka ce gwamnatin Nijar din tana sanya kafa tana take dokokin kasa da na kasa da kasa da ta sanya ma hannu.
Your browser doesn’t support HTML5