Watan Disamba Na Kowace Shekara Na Zuwa Da Abubuwa Da Dama

Daga Hagu zuwa Dama: Comrade Danjuma Bello Sarki, Shugaban Matasa na yakin neman zaben gwamna Yero da Bajoga a karkashin tutar jam’iyar PDP a Giwa, jahar Kaduna, da Shugaban Matasan jam’iyar PDP na Kaduna ta tsakiya: da Shugaban Matasan jam’iyar PDP na ja

Watan Disamba na kowace shekara watane da kan zo da abubuwa da dama, a cikin watan ne ake bukin Kirsimas, haka kuma wantan da shekara ke karewa ne. Don haka ana kara kiran matasa da su kokarta wajen ganin sun kaurace ma duk wasu abubuwan da zasu tada zaune tsaye.

Masana na ganin cewar duk wasu abubuwa na rashin zaman lafiya akanyi amfani da matasa ne wajen aiwatar da su, shiyasa hukumomi a matakin jihohi ke gani akwai bukatar mutane su guji aiwatar da kowane irin taro, batare da izini ba musamman a cikin wannan watan na disamba.

Ganin cewar karshen shekara tazo, akwai bukatar mutane su tsara ma kansu wasu abubuwa da zasu bukaci cinnma a cikin shekara mai shigowa. Wasu daga cikin hanyoyi da ya kamata ace matasa subi don kaiwa ga tudun tsira shine, su duba irin abubuwa da sukayi a cikin shekarar da ake ciki, wane irin abun cigaba suka yima kansu a cikin tsawon shekarar, hakan zai basu damar sake kudurta wasu abubuwa da zasu nemi cinnma a cikin shekara mai zuwa. Yin hakan zai basu damar fahimtar rayuwa.