Mr. Adewale Adeyemo, haifafen Najeriya ne, wanda ya kafa tarihi a duniya. Tarihin kasar Amurka bazai taba cika ba batare da fadan sunan shi ba. Kasancewar ya zamo mutun na farko dan kasar waje da ya taba rike matsayin mataimakin mai bama shugaban kasar Amurka shawara a harkar tsaro da tattaalin arzikin kasa-da-kasa.
Shugaban kasar Amurka Baraka Obama, ya bayyanar da Mr. Adewale, a matsayin wani mutun da ya taimaka kwarai wajen farfado da tattalin arzikin kasar a dai-dai lokacin da duniya ta shiga rudanin tattalin arziki a shekarar 2008.
A dai-dai lokacin kaddamarwar shugaba Obama ya dafa kafadar Mr. Adewale, ya kuma kirashi da wani suna “Walley” shi dai Adewale yayi aiki a ma’aikatar kudi ta kasar Amurka, da har ya kai babban ma’aikaci, yanzu haka ya gaji kujerar mai bada shawarar ne a fannin tsaro daga Caroline Atkinson.
Mr. Adewale, dai ya taka rawa so sai a wajen taron canjin yanayi da aka gudanar a kasar Paris, inda ya wakilci kasar Amurka, hakama da duk taron da ake gudanarwa na kasashen da sukafi karfin arziki a duniya, da ake kira G 20.