An Haifi Jariri Da Sinadarin Haihuwa Mafi Yawan Shekaru A Duniya

Mom and Dad

Kunding tattara abubuwan tarihi na duniya wato “Guinness World Record” a turance, sun bayyanar da wani abu da ya shiga cikin tsarin abubuwan ban-mamaki a duniya, da wani mutun dan kasar Australia ”Mr. Alex Powell, yayi.

Tun bayan wani bincike da likitoci suk gudanar a kan Mr. Alex, lokacin da yake dan-shekaru 15, da cewar yana da wata cuta da take a cikin jinin jikin shi, mai suna "Hodgkin's lymphoma" a turance. Ita dai wannan cutar idan tayi yawa a cikin jikin mutun, tana iya haifar mishi da nakasa da dama. Daya daga cikin abun da take iya haifarwa itace, mutun kan iya rasa kuzari da karfin sinadarin iya haihuwa. Tun bayan bayyana mishi hakan, sai yayi tunanin ya dibi sinadarin haihuwar jikin shi wato “Sperm” wanda ya ajiye shi har tsawon shekaru 23, kamin ya bada shi don sawa ga matar da ya aura, kuma wannan sinadarin da aka hada da na matar shi bayan watannin 9 sun samu haihuwar yaro.

A ranar 17 ga watan Yuli na wannan shekarar aka haifi wannan jaririn, da sinadarin haihuwar shi yafi kowannen dadewa a duniya, batare da yana cikin jikin uban yaron ba. Domin a kasar Ingila antaba ajiye irin wannan sinadarin amma shekarun wannan 21, hakan yasa wannan yafi ko wannen dadewa a duniya. Bayanai dai sun nuna cewar an ajiye sinadarin a wani mazubi mai tsafta da inganci, kuma aka sa shi cikin firiji mai kankara har na tsawon waddannan shekarun.