Kabilar "Toraja" A Kasar Indonesia "Gawar Mamata" Abun Kaunace

Gawa

Kusan za’a iya cewa a kowace kasa, kabila ko al’ada, a fadin duniya, mutane kanji tsoron gawa, koda kuwa gawar masoyan sune. Idan har mutun ya mutu koda kuwa mata, miji, da ne za’a ga cewar mutane na kokarin rabuwa da gawar, ba zasu bukaci kusantar wannan gawarba.

Amma a kasar Indonesia, wasu kabilar Toraja, a yankin kudancin Sulawesi, sukan ajiye gawar mamata har na tsawon wani lokaci, wanda suka dauki hakan a matsayin karramawa. A irin tasu al’adar mutunta mutun bayan ya mutu shine a barshi a cikin al’umar shi, da za’a dinga gudanar da bukukuwa daga lokaci zuwa lokaci na tunawa da shi.

A duk bayan shekaru uku 3, sukan haka kabarurukan masoyan su, su dauko kasusuwan su suyi musu wanka da kwalliya, har da sa musu sababbin kaya, ai musu ado, kana a zagaya dasu lungu da sako na kauyukan su. Hakan dai sun bayyanar da shi a matsayin hanyar karrama masoya mamata. Wannan shine Allah daya gari ban-ban.