Shekarun Kuruciya Ne Dai-Dai Lokacin Tsarin Rayuwa!

Sau da dama matasan kan ga cewar da zarar sun kammala makaranta walau, makarantar sakandire ko jami’a, sai suga kamar sun gama komai. Alhali kamata yayi su sani cewar kammala karatun jami’a bai zamana cewar mutun ya cinma komai a rayuwar shi ba. Hakanma na nunacewar akwai sauran rina a kaba. Masana na gani cewar daga lokacin da mutun ya kammala karatu ko wani abu da ya sama kanshi burin yi, to daga wannan lokacin zai fuskanci wasu sauran kalubale na rayuwa.

Don haka matasa nada bukatar waiwayar wasu abubuwa a rayuwa don tabbatar da tsayuwar su a hanya madai-daiciya. Abu na farko da ya kamata a duba shine, mutun nada sauran abubuwa da zai koya a rayuwa daga randa akace ya bar makaranta, don kuwa wasu abubuwan ba a makaranta ake koyon suba.

A duk lokacin da mutun yayi alkawali ya kamata ya kokarta wajen cika alkawalin koda kuwa zai sa kanshi cikin matsatsin hali. Da yawa idan mutun yayi alkawalin zuwa wani guri, da bai samu isa da wuri ba, sai ya daura laifin ko dai mota ta lalace ko ya samu shiga cikin gosulo. A dia-dai wannan lokacin abun da yafi kamata shine mutun ya fadi gaskiya.

Mafi akasarin mutane basu so a bayyana musu wasu kurakuran su ko abubuwa da sukayi bisa kuskure, musamman idan wannan abun yayi dai-dai da ra’ayin su. Duk kuwa wanda ke da bukatar cinma nasara a rayuwa to akwai bukatar ya dinga sauraron masu sukar wasu abubuwa da yake aikatawa, da kuma daukar su da kunnen basira don canzawa da kuma kallon wadannan mutane a matsayin masoya gare shi ba makiya ba.