Mutane da dama kanyi mamakin yadda aka ajiye “Cake” har na tsawon shekaru dari 100. Babu abun mamaki, domin kuwa wasu iyaye sunyi wani shiri don kaima wannan mataki. Mr. Ronald Warninger, mai shekaru sittin da bakwai 67, ya gano wata ajiya da mahaifan shi su kayi.
A lokacin da yake gyaran gidan da mahaifan shi suka zauna na tsawon shekaru, wanda a gidan aka haife shi. Ya ga wani mazubi da ake kira “hatbox” a cikin wani firij, koda ya bude mazubin sai yaga ashe Cake ne. Kuma wannan cake din tun na auren kakar shi ne, a lokacin auren mahaifan iyayeyn shin, kimanin shekaru 100, da suka wuce.
Yace yana iya tuna lokacin da yake yaro, iyayen shi sun saka wannan mazubin a cikin firij, kuma suka gaya mishi cewar kada ya taba. Tun bayan wasu lokutta sai ya dena ganin mazubin, don haka bai tambaya ko yana ina ba. Amma a wannan watan Maris shekarar 2015, sai gashi ya sake ganin mazubin, koda ya bude sai yaga ashe cake ne wanda kakannnin shi suka ajiye don tarihi, har suka mika shi ga iyayen shi, gashi shikuma ya kaiga rike cake din, duk bayan shekaru 100.
A ranar 17 ga watan Maris, 1915, itace ranar da kakannin na shi su kayi aure, kuma sun dau alwashin idan har Allah yasa suna raye suka kai shekaru dari 100, zasu yi bukin cika shekara dari 100, dayin auren su. Basu kai wannan lokacin ba, amma ‘yayan su da jikokin su, sun ga wannan ranar domin kuwa koda aka daukko wannan cake din, babu abun da ya same shi, yana nan kamar yau akayi shi. A cikin mazubin da aka ajiye shi, anga wata wasika da abokin ango ya rubuta mishi a lokacin auren duk an ajiye su tare.