Gizo-Gizo Ya Haddasa Rudani Tsakanin Kamfani Da Kwastoma

BRITAIN/

Wani lauya mai zaman kanshi a kasar Ingila, Mr. John Hogg, ya shigar da karar kamfanin jirgin “Qatar Airline” na kasashen daular larabawa. Dalilin shi kuwa shine, a lokacin daya ke cikin jirgin a kasar Afrika ta kudu, wani Gizo-gizo ya cije shi, wanda ya kusa yin sanadin rabuwa da kafar shi.

Yace a lokacin da suke cikin jirgin, yaga gizo-gizon, wanda wasu mutane su kayi ta ihu cewar ga gizo-gizo, a wannan lokacin gizo-gizon ya fito daga kasan kujerar shi, amma a wannan lokacin baiji wani cizo mai zafi ba, sai bayan kwana daya kafar shi ta kumbura kamar ba tashi ba.

Da ganin haka ya garzaya asibiti inda akayi mishi aiki a kafar sau uku, kuma ya ga likitan fata, likitocin sun gaya mishi cewar kadan ya rage da ko yarasa kafar ko kuma ya mutu saboda tsanananin dafin wannan gizo-gizon. Yanzu dai yana bukatar kamfanin jirgin su biyashi duk kudaden daya kashe a sanadiyar cizon kwaron, domin kuwa da sun dauki lafiya fasinjojin su da mahimanci da sun tabbatar da magance duk wata hallita da zata cutar da mutane kamin shiga jirgin.