Allah mai hallitta daban-daban wani mutun mai suna Muhibija Buljubasic, yana da karfin rike duk wani karfe a jikin shi. Ya bayyanar da wannan a matsayin wata baiwa da Allah ya hallice shi da ita. Domin kuwa idan aka saka duk wani abu dangin karfe yana iya zama a jikin shi batare da an rike shiba, haka ma wayar hannu da rimoto na tibi, duk suna iya zama a jikin shi, wanda sai ansa karfi kamin a iya cire su.
Sai wata mata ‘yar-kasar Gemany, Michele Koebke, ta horar da jikinta wanda take da kunkuru da yafi kan-kanta a duniya, mafi akasarin kunkuru na kowane mutun babba yakan kai girman inci 25, amma nata ya koma inci 16.
Haka Francisco Domingo, shine mutun na farko da yafi kowa katon baki a duniya, domin kuwa yana iya saka gwan-gwanin Coca Cola ta kwance a bakin shi kuma ya rufe, haka yana iya daga leben shi har zuwa goshin shi. Wanda ba kowa zai iya wannan abun ba.