A shekarar 1955, aka fara kera mota mai budaden sama wato “Corvette” ana dai iya bude irin wadannan motocin ta sama don shan iska. A wannan shekarar an kir-kiri guda 700, a shekarar 1953 kamfanin Vintage ya kir-kiri guda 300.
Wata mata da ta mallaki daya daga cikin irin motocin masu bude sama, tun a wancan lokacin yanzu ta fitar da tata motar don sayarwa, an taya motar a kan $3,500 dai-dai da naira milliyan daya. Ta bayyanar da wannan motar a matsayin wata kyauta da iyayen ta suka siya mata a wancan lokacin.
Yanzu haka dai mutane da dama sun yadda su siya motar, don tarihi da motar keda. Tace tana iya tuna yadda kalar mutar take a wancan lokacin, amma bazata iya tuna ya kalan cikin motar ya keba, don ta canza ma motar fyanti. An dai bayyanar da wannan motar a matsayin wani abun tarihi da mutane da dama zasu so sugani don ganin yadda mutane da ke tunani. Hakan na iya bama mutanen yanzu damar kara kuzari wajen kir-kirar abubuwa da cigaba na irin wannan zamanin.