Kowane yaro da Allah, ya hallita yana da baiwa dai-dai da kowa, haka kuma basira ta kowa tana iya bayyana ne idan yaro ya maida hankali wajen koyon wani abu da yake sha'awa. Kana da nuna naciya wajen koyon wani abu da yaba da sha'awa, haka da lura da wasu abubuwa da wasu yaran matasa keyi a rayuwar su. Hakan yasa wasu matasa masu kananan shekaru a nan kasar Amurka, sun shiga wata gasa inda su kayi nasara da wasu abubuwa da suka kir-kira kuma suka samu lambar yabo.
Anish Singhani, dan shekara goma sha uku 13, yayi amfani da fahasarshi ta ganin taimakama mutane masu mutuwar jiki. Anish ya kera na’ura da hanyar amfani da ita domin bada umurni ga kujera mai daukar mutane masu lalurar. Wannan matashin yana mai fatar na’urar data amfani mutane ta kuma kawo saukin rayuwa ga masu lalurar.
Avery Clowes, dan shekara goma sha uku 13, ya gina injim ya kuma gwada yadda za’ayi amfani da ruwa mai gudana domin samun wutar lantarki. Avery, yayi amfani da sanannen gwanjin da aka tsara tun karnin daya wuce da Lord Kelvin’s yayi. Wannan gwajin ya samarda wutar lantarki daga wayar karfe da gudanar ruwa dake fita daga bokitayya guda biyu. Matashin yayi korafin da cewa zai iya kula da adadin lantarkin dake samuwa ta wannan hanyar ta kula ko canza yadda ruwan ke gudana daga bokitayyan.