Na Samu Ribar Abu 3 Duk A Sanadiyar Neman Ilimi A Duniya

Bashir Umar Hassan

Bashir Umar Hassan, matashi dan Najeriya da ke karatun digiri na biyu a kasar Amurka, ya bayyanar da irin banbance-banbance da ake dashi a tsakanin kartun Najeriya da na kasar Amurka. Yana ganin kamar yadda tsarin karatu yake a kasar Amurka idan da haka yake a kasar Najeriya, to lallai da ba shakka da duk kowa ya ilmanta a gida Najeriya.

Ya zo kasar Amurka, inda ya fara karatun digiri na farko, kuma bayan ya kamala digirin farko a bangaren Tsimi da tanaji cikin lissafi wato "Accounting" a turance, yanzu haka yana karatun digiri na biyu a bangaren kimiyyar bayanai."Masters in Information Technology" Haka kuma yana ganin ba komai yasa ya samu wannan nasarar ba illa yadda ya maida hankali a lokacin da yake karatun sakandire a gida Najeriya.

Don haka yana ganin cewar idan har shi zai samu damar zuwa kasar Amurka, don karatu, to lallai kowane yaro na iya samun wannan damar, musamman ma idan ya maida hankali a lokacin da yake karatun sakandire. Don a gaskiya karatun firamari da sakandire sune jagororin duk wani kararu, da mutun zaiyi a duniya, idan akace mutun yasamu wadannan karatun nagartatu, to lallai zai iya samun nasara a kowane irin karatu.

Haka kuma duk a cikin irin nasara a yasamu a karatun shi a kasar Amurka, wanda yake ganin cewar yasamu riba uku, baya ga karatu, sai sanin makamar aiki, sannan uwa uba Allah ya hada shi da masoyiyar shi, wanda yanzu har sunyi aure, suna cikin farinciki da kwanciyar hankali. Haka suna fatar su samu damar kamala karatun su, wanda daga nan saisu koma gida don taimaka ma ‘yan’uwa matasa da daukacin kasa baki daya.