A duk lokacin da akace matasa basu da tunanin kan su, sai abun da wani yayi musu tunani akai, to shine ake samun al’umah da bazata zama wani abu a rayuwa ba. Domin kuwa yadda matasa ke tashi tsaye wajen neman ilimi da neman abun duniya a nan kasar Amurka, ya banbanta da yadda akeyi a kasashen Afrika.
Tsarin makarantu a matakin farko a kasar Amurka, ana koyama yara cewar suna da tasu irin gudunmawa da zasu bada a wajen ciyar da kasa gaba, don haka kowane yaro yasama ranshi cewar shine, wanda zai kai kasar mataki nag aba. Hakan yana sa yara su fara tunanin menene zasu yi don ayi fahariya dasu a yankin su da daukacin kasar su baki daya.
Wannan shine irin tunani da yakamata ace kowane matashi yayi, musamman ma wadanda suka kamala karatun firamari, su fara tunanin mai zasu yi a gaba wanda zai haifar da cigaba a kasar su. Kana Mr. Yunana Ahmed, ya cigaba da cewar duk matashin da ya kammala karatun sakandire, kuma yasan abun da ya keyi, to babu shakka idan ya shiga jami’a zai samu abubuwa cikin sauki.
Hakan kuma zai bashi damar samun gurbi don zuwa kasar waje don karo karatu. Domin kuwa akwai kungiyoyi da dama da suke kokarin daukar yara daga kasashen Afrika su kaisu wasu kasashe da suka cigaba a duniya don karo ilimi, wanda shima ta haka ya samu zuwa kasar Amurka. Babu abun da bai yuwa sai dai, idan mutun kawai bai sa kanshi ba.