Duk Matashin Da Ya Yarda Da Kanshi! Zai Zama Zakara A Rayuwa

Yunana Ahmed 2

Yunana Ahmed, haifaffen garin Das, wanda kuma yasamu damar zuwa kasar wajen don karatun digirin digirgir a nan kasar Amurka, ya bayyanar da cewar shi ba dan kowa bane, iyayen shi manoma ne amma saboda sanin muhimancin ilimi, yasa iyayen shi sun kashe kaso mai yawa na abun da suka mallaka suka sasu makaranta.

Ya kara da cewar babban abun da yasa wasu matasa basu maida hankali wajen neman ilimi a kowane mataki, ba komai bane illa yadda ba’a bama matasan gwarin gwiwa, na neman ilimin don zama wani abu a rayuwa. Suku kuma matasan basa lura da yadda wasu abubuwa ke gudana a rayuwar yau da kullun.

Haka kuma sau da yawa matasa sukan maida kansu baya, da tunanin cewar komai sai gwamnati tayi ma mutun kamin yayi tunanin yima kanshi, hakan shike kara maida komai baya. Domin kuwa da ya tsaya da irin wannan tunani, to da yanzu bai kai inda yake ba. Yana iya tunawa lokacin da suka gama sakandire, abokan shi da yawa basu cigaba ba, yanzu haka dai yana kokarin kiran matasa da susan da cewar, sai sun tashi tsaye kamin wani abun alkhairi ya kawo kansu koda kuwa daga gwamnatin ne.