Soyayyar "Tiger Wood" Da Bazawarar Shi Ta Sake Zani

Tiger Wood

Tiger Wood, shahararen dan wasan kwallon rami ne, da yayi fice a duniya. Wato tarihin kwallon rami “Golf” a duniya ba zai cika ba idan ba’a ambato sunan Tiger Wood ba. Tun bayan wasu shekaru da ya samu wata matsala da matar shi ta farko, kuma maman ‘yayan shi, wanda yakai su ga rabuwa batare da jin dadi ba.

Hakan ya shafi rayuwar dan-wasan matuka, don tun bayan hakan abubuwa suka fara canza mishi. Bayan nan ya sake shiga cikin wata soyyaya da wata bazawara Lindsey Vonn, amma bayan shekaru uku 3, cikin soyayyar su, sun rabu. A lokacin da manema labarai suke zantawa da bazawarar ta shi, ta bayyanar da tarayyar ta da Tiger a matsayin abun da bazata taba mantawa ba, domi kuwa taji dadin zama da shi.

Amma a matsayin ta na mace da bata, taba soyyaya ba tun tasowar ta, domin tsohon mijin ta shine saurayin ta na farko, amma daga mutuwar aurenta, ta shiga wata sabuwar soyayya don haka tana ganin hakan ba shine abu da ya dace da ita ba. Yanzu dai tace tana da bukatar ta sake haihuwa, don itama ta fito daga babban gida, sai dai yanzu abun da tasa a gaba shine, ta cinma burinta na zama zakara a wasan tseren dusar kankara, wanda zata fara shiri yanzu kamin shekarar 2018.