Mace Da Tafi Karfi A Duniyar "Boxing" Tasha Kaye A Karon Farko

Ronda Rousey

Ronda Rousey, shahararriyar mai wasan “Boxing” ce wadda kuma ba’a taba yin nasa a kanta ba, amma a shekaran jiya Lahadi a karon farko Rousey, ta sha kasa. Kimanin awowi kadan bayan samun nasar da akayi a kanta, ta bayyanama magoya bayanta a shafin ta na Instagram cewa “Ina so nayi amfani da wannan damar na gode muku da goyon baya da kuke bani, kuma na gode da yadda kuka nuna damuwa da lafiya ta, amma ina lafiya”

Wannan wasan dai ya bama dubun dubatan mutane mamaki, ganin cewar ba’a taba bata kashi a wasa ba, amma a karon farko cikin kasa da minti daya daga shiga zagaye na biyu, sai kawai aka kawo kashen wasan. Ta kara da cewar “Dama tun a baya na fada cewar ina da bukatar na dauki karamin hutu, amma zan dawo”

Rousey, dai ta bar filin wasan a kasar Australia, jim kadan bayan bayyar da abokiyar hamayyar ta a matsayin wadda tayi nasara, kuma wadda itace mace mafi karfi a fadin duniya yanzu. An garzaya da Rousey, din dai asibiti don duba lafiyar ta da kuma yi mata dinki a leben ta. Tun dai kamun wannan wasan ta bayyanar da cewar, tana da bukatar hutu don ta samu ta kamala fim dinta, mai take “Mile 22” Kuma zata dawo a shekara mai zuwa 2016.