Shafufukan Yanar Gizo Na Iya Taimakawa Wajen Bincike Da Dama

FILE - A portrait of the Twitter logo in Ventura, California.

Tun bayan tashin wasu bama-bomai da harbe-harbe da akayi shekaran jiya a kasar Paris, mahukunta na daukar wani sabon salo don gano mutane da abun ya shafa, da kuma wadanda suka aikata wadannan ta’asar.

Mahukunta sun fito da tsarin amfani da shafin zumunta na yanar gizo, da suka hada da shafin “Twitter, facebook” sun ce domin mafi akasarin wadanda abun ya shafa matasa ne, wadanda suke da sha’awar waka, sun halarci wuraren ne don nishadi, kuma akasarin matasan, sunyi amfani da shafufuka na yanar gizo wajen saka hotunan su da bada bayanan halin da suke ciki na annashuwa, ga yan'uwan su da abokan su.

Don haka amfani da wannan fagen wanda matasa sukayi amfani dashi da ya fara da #rechercheparis, zai taimaka matuka, wajen gano wadanda suka mutu da raunana. Ana tsammanin kimanin sama da mutane dari da ashirin da takwas 128, ne suka rasa rayukan su a wajen. Akasarin matasan da suka mutu a wajen masu shekaru a tsakanin 20 – 30 ne, akwai wadanda suka bace masu shekaru 12 da 13. Masana na ganin cewar amfani da yanar gizo wajen binciken ayyukan ta’addanci, wata hanya ce mai sauki da kuma zata bada sakamako cikin gaggawa. Don haka matasa su san me suke rubutawa a shafufukan su.