Shararen kamfanin da a kafi sani masu kera kwamfutoci wato “Microsoft” sun kir-kiri wani sabon agogon hannu da ke abubuwa fiye da duba lokaci. Wannan agogon ana kiran shi “Microsoft Band” a turance, baya ga duba lokaci, duk mai wannan agogon zai iya amfani da shi don duba lafiyar jikin shi.
Mutun kan iya duba yadda zuciyar shi ke buguwa a kowane lokaci, wanda idan mutun yaga wani abun da yawuce hankali sai ya dauki mataki na gaba. Kana mutun zai iya duba irin yadda jikin shi ke kona wasu abubuwa da yaci da basu da amfani ga jikin shi, haka kuma ana iya duba inganci bacci da mutun yayi duk da wannan agogon.
Kana mutun kan iya amfani da wannan agogon, don gani yawan lokaci da yayi yana tafiya da kafa, ko gudu da tseren keke, da wasu wasanni. Agogon na kuma dauke da wasu na’urorin haska bayanai goma sha daya 11, wanda suka hada da tsarin kai ni gida a ko ina mutun yake, da fitila mai ganin kwakwam, da dai sauran su. Yana nuna abubuwa a cikin kalar su yadda suke. Haka kuma ana iya hada wannan agogon da wayar hannu ta kamfanin Microsoft, da wayar Androide, harma da ta IPhone. Kudin agogon ya kai dalar Amurka $250 dai-dai da naira dubu hamsin da biyar 55,000.