Dan-Najeriya Ya Kir-Kiri Mutun-Mutumi "Robot" A Amurka

Almustapha Almustapha

Kadan daga cikin tarihin Al-Mustapha Al-Mustapha, ke nan wanda ya kirkiri Mutun mutumi wato “Robot” Tun ina makarantar firamari na kasanche mai sha’awa da hazaka ga kimiya. Hazakata ta saka daga aji hudu na firamari aka sanyani aji shidda kuma aka zabe ni chikin jigogin makaranta daga chikin dalibai wato da turnachi Prefect. Bayan na kare firamari sai na shiga makarantar sakandire ta Sultan Bello inda na kare matakin kasa na secondary school wato Junior Secondary School (JSS).

Asali dama a lokachin shiga zangon manya na secondary school wato Senior Classes makaranta takan tantanche daga sakamakon jarabawar wadanda zasu karanta bangaren kimiyya “Science” koko Social Sciences. Ta hakan na samu nasarar shiga ajin kimmiya. Bayan na fara na samu canjin makaranta zuwa “Supreme international College Kaduna” inda na kammala karatuna nasamu nasarar jarabawar secondary a shekarar 2007. A lokachin na rubuta jarabawar shiga jami’a kai tsaye sai dai maki na bai kai matakin maki na dauka jami’a ba. Lokacin ne bayan na koma Sakkwato na cika form din karatun share fagen shiga Jami’ar Usmanu Danfodiyo (Matriculation)

Na samu damar shiga jami’a don karantar “Physics” domin shine yafi can canta dani daga sakamakon jarabawa ta. Nayi murna matuka domin inason “physics” kuma ina fahimtarshi sosai. Ina chikin zangon farko ne na jamia’a (UG1) Amma ana haka sai na samu damar zuwa kasar Amurka don karatu, Inda karatun zai kasanche kashi biyu shekara biyu na farko “Associate Degree” na biyu na karshe “Degree”.