Canjin Yanayin Warin Jiki Nada Alaka Da Cutar "Parkinson"

Ağrı Kesici Hap Parkinson Riskini Azaltıyor

Matar wani mutum wanda ya sha wahala tare da cutar “Parkinson” ta jawo hankali akan sabon bincike, a wannan makon a cikin yanayi bayan da ta gano ta iya gane cutar da ta kashe mijinta ta wari. Ita dai cutar, yadda ake iya gane ta, shine za’a ga jikin mutun na rawa a kowane lokaci, mutun baya iya rike abu a hannun shi, ko kuma zai dinga yin abubuwa a cikin sanyin jiki.

Joy Milne, mai shekaru 65, ta shaida wa masu bincike cewa ta lura da wani canji a cikin wari jikin marigayin mijin ta, shekaru kafin ya ɓullo da bayyanar cututtuka na “Parkinson” tana nufin cewar idan yanayin warin jikin mutun ya canza daga yadda ya saba da shi shekaru da dama, to akwai bukatar mutun ya ga likita don tantance mai yasa hakan.

Ada ita wannan cutar tafi yawaituwa ga mutane masu yawan shekaru, amma a yanzu tafara sauka ga masu kananan shekaru. Don haka ta jawo hankalin mahukunta da a zurfafa bincike a kan wannan cutar.