Yarinya 'Yar Shekaru 12 Ta Kir-Kiri Na'urar Tallafawa Rayuwar Kifaye

Audrey Glende

A kowace shekara, wata gidauniya da ake kira “Society for Science” da gidauniyar Jama'a ta kasa da kimiyya, suna gudanar da gasar dalibai ‘yan aji shida, bakwai, da takwas a kasar Amurka.

A gasar, da ake kira “Broadcom Math” wadda ta kunshi fannin kimiyya da fasaha, kere-kere. Akan fitar da zakaru a kowace shekara. A kowace shekara akan fitar da mutun biyu wadanda sukayi rawar gani. Kana akan bada kyautar kudi ga wanda yazo na farko, da suka kai dallar Amurka $ 25,000 dai–dai da naira milliyan fiyar da dubu dari biyar 5,500,000.

A shekarar bana wata yarinyar mai suna “Audrey Glende” ‘yar shekaru goma sha biyu 12, ta kir-kiri wata na’ura da zata ceto rayuwar kifaye. Ita dai yarinyar ta fito da wata hanya da za’a dinga fitar da kashin kifi, a cikin wani mazubin kifaye da ake sakawa a daki don kayatarwa, wanda ake kira “Aquarium” a turance. Domin ta iya fahimtar cewar, idan ba'a fitar da kashin kifayen a cikin ruwan tunda ruwan baya zuwa ko'ina, yana kashe su. Don haka ta fito da wata sabuwar dubar da za'a fitar da kashin cikin sauki.