WASHINGRON DC, —
An gudanar da gasar Gemu da Gashin Baki na duniya a kasar Austria. Ana dai gudanar da wannan gasar ne kusan duk bayan wasu ‘yan shekaru. Duk dai da hakan, a kowace shekara akan samu masu shiga gasar daban-daban, kuma akanyi gasar a wurare da ban.
Abu dai da baya canzawa a kowace shekara shine, yadda mutane ke kawatar da gemun su, ko gashin bakin su, ta yadda zai bada sha’awa da ma’ana. A wannan shekarar dai wannan matashin shine ya lashe gasar. Sai kuma wata shekara kuma za'a sake zaban wanda yafi kayatarwa.