Ga dukkan iyaye da ke da ‘yaya “Wada” babban abun burin su a rayuwa shine suga wadannan ‘yayan nasu sun zama cikin farin ciki da annashuwa kamar sauran yara. Yana da ban tausayi idan aka haifi yaro da wata nakasa kowace iri ce, wanda a wasu lokkuta yara ‘yan-uwan su kan maida su abun dariya ko magana.
Hakan yakan sa yaran cikin damuwa, wanda daga karshe ma basu sanin lokacin da sukanyi wani abu, da zai iya sa rayuwar su cikin hadari. Don haka akwai bukatar iyaye su dinga kula da irin yadda wadanan yaran ke gudanar da rayuwar su ta yau da kullun.
Mr. Paul da matar shi Kerry, suna da yarinya Jillian, wanda take wada, ta samu damar kamala karatun jami’a, tana da shekaru 25. Amma kullun tunanin su ya za’ayi tasamu miji, tayi aure kamar sauran yara. Rana daya kawai sai ga Jillian ta kawo wanda zata aura, shima wada. Mr. Paul, baban Jillian, ya rubuta mata wasika a ranar auren ta.
Zuwa ga ‘yata Jillina, tun bayan haihuwar ki, kullun damuwar mu itace wanene zai yadda ya aure ki, ganin cewar kina da hallita daban da ta sauran yara. Amma yau gashi munga auren ki, duk da irin hallitar da Allah, yayi miki baki zama mai matattar zuciya ba, kin tashi tsaye wanda yau muna cike da farin ciki. Ashe dai duk wanda Allah, ya hallita yayi masa guzurin sa a duniya. Don haka babu maraya sai raggo. Muna kara fahariya dake da kuma duk wadanda Allah, yayi su da wata nakasa a fadin duniya.