Wani Jirgin Ruwa Da Ya Bace Ya Bayyana Bayan Shekaru 150

An gano farfelar wani jirgin ruwa dake dangare da kaya dauke kuma da mutane, da ya bace a cikin ruwa, shekaru dari da hamsin 150, da suka wuce. Wannan jirgin dai na dauke da kaya, wanda za’a kai jihar Ohio daga jihar New York a watan Nuwamba ta shekarar 1862.

Tun a wannan shekarar akayi ta neman wannan jirgin, tun bayan tashin jirgin, wata iska ta taso mai karfi da tayi sanadiyar halakar jirigin. Jirgin ya nitse cikin karkashin kasa, da yakai kimanin murabba’in tafiyar kilomita dari da hamsin da biyar 155.

Wasu mutane da suka fara neman jirgin tun a shekarar 1970. Sun kwashe kimanin shekaru arba’in da biyar 45, suna neman jirgin. Amma sai a wannan watan aka gano jirgin. Masu binciken sunce wasu daga cikin bangarorin jirgin, basu matsa daga inda jirgin ya nitse ba tun a wancan lokacin.