WASHINGTON DC, —
A cewar wata kungiyar wasu mabiya addinin kiristanci, a garin Philadelphia, ta nan kasar Amurka, ranar 7 ga watan Oktoba ta wannan shekar ce ranar karshen duniya.
Amma dai haryanzu ga mutane a raye, irin haka yasha faruwa, ko ace wasu mutane a shekaru da dama sun ta fadin irin hakan, amma har wazuwa yau hakan bai faruba. A kasar Ingila, masu ilimin taurari, sun yi wani harsashen dake nuni da cewar za’a samu ambaliyar ruwa wanda zai yi sanadiyar zuwan karshen duniya.
A watan Mayu na shekarar 1780, wasu kungiyoyi a kasar Ingila, sunyi harsashen karshen duniya zai zo, a sanadiyar wata matsananciyar dusar kankara. Amma duk da wadannan harsashen haryanzu babu wata alama ta karshen duniya.
Don haka ina mafita mutane?