Bisa ga al’ada ta kasar Amurka, a lokacin buki bangaren ango da na amarya sukan hada kudi, wajen shirya liyafar buki. Wasu ango da amarya sun shirya bukin su, wanda har sun zabi Otel da za’aje don gudanar da buki. Don kayatar da bukin sun tafi Otel da ke da tsada, suka biya kudin abincin mutun dari da ashirin 120, wadannda suka gayyata.
Angon da Amaryar sun biya kudi dalar Amurka dubu talatin da biyar $35,000 kimanin naira milliyan bakwai da dubu dari biyar 7,500,000. Don karrama baki. Wanda daga bisani, za’a aiko musu da sauran kudin da zasu biya bayan bukin. Abun mamaki, ana cikin sha’ani a dai-dai lokacin cin abinci, sai Angon yace anfasa buki.
Cikin fushi ita kuwa Amaryar sai ta gayyato mutanen anguwa da basu da abinci ko gida don su zo suci abinci da akayi don baki, a ranar murnar auren su. Amma abun tambaya a nan shine wai idan kai ne ko kece haka yafaru da mai zakuyi?