Hadarin Jirgin Sama Yayi Sanadiyar Mutuwar Wasu Mutane Biyu

Hadarin jirgi

Mutane biyu ne suka mutu cikin wani hadarin jirgin sama da aka samu a jihar North California, ta nan kasar Amurka. Jirgin saman ya dai fadi ne kusa da wani gida, jim kadan bayan tashin shi sama. Kadan bayan faduwar jirgin wuta ta tashi, amma anyi nasarar kashe wutar, gidan dai na kasa da mil kadan daga filin jirgin sama. A cikin wani dan karamin kauye mai yawan itatuwa jirgin ya fada ma da misalign 5:40 na yamma.

Maja Smith, wata mai binciken hadduran jiragen sama ne, ta hukumar “Transport Safety Board” tace jirgin saman na dauke ne kawai da mutane biyu. Ta kara dacewar, ba ta san sunayen wadanda ke tuke da jirgin saman ba, kuma ba a san daga ina suke ba, balle a san ina zasu. Yanzu haka dai ana cigaba da tsananta bincike don gano suwaye a cikin girgin.

A tabakin wata mai kula da gidajen hutu da jirgin ya abkawa, Gingar Nicolay-Davis, tace mutane biyu da karen su, sun samu damar fita daga gidan, batare da sun samu wata matsala ba. Ta kara da cewar suna zaune cikin gidan sai kawai su kaji abu daga sama ya fado.