WASHINGTON DC, —
Shugaban gidan namun daji wato gidan “Zoo” na kasar Malawi, ya bayyanar da cewar Giwa da Kada sun kashe kimanin mutane bakwai 7, a lokutta da ban-da-ban cikin sati bakwai 7.
Daya daga cikin wajen kallon namun dajin na “Liwonde National Park” ba zagaye yake ba, don haka mutane kan shiga a kowane lokaci, wanda sau da yawa ma mutane kanyi barna a ciki. Don haka sabon kamfanin da ya dauki nauyin kula da yankin, na kokari wajen ganin a inganta dajin. A yanzu dai ana kokarin zagaye wajen, wanda yake da nisan kilomita dari da talatin “130-Kilometer.”
Hudu daga cikin muta nen da suka mutu, kada ce ta kashe su, daya kuwa giwa, sai sauran mutun biyun kuwa, suma kada ne tayi sanadiyar mutuwan su, a yankin kusa da gidan kallon namun dajin.