FIFA Ta Dakatar Da Jack Warner Har Abada

Fifa

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta tabbatar da dakatar da Mr. Jack Warner, daga duk wata harka da ta shafi kwallon kafa har karshen tsawon rayuwar shi. Biyo bayan bincike da aka gudanar a kan yadda aka gudanar da shiryar da wasan kwallon kafar duniya na shekarun 2018 da 2022.

Shi dai Mr. Warner, ya kwashe shekaru ashirin da daya 21, yana shugabantar kungiyar kwallon kafar kasashen yankin arewa, tsakiyar Amurka da kasashen yankin kudanci (CONCACAF). Yana daya daga cikin manyan jami’an da aka kama a kasar Geneva, a watan mayu cikin wani bincike da hukumar binciken manya laifufuka ta Amurka FBI ke gudanarwa.

An dai yi matsaya ne bayan sakamakon binciken da aka gudanar dangane da irin cin hanci da aka bayar lokacin, zaben kasashen da zasu dauki nauyin kwallon kafar duniya da za’a gudanar a shekarun 2018 da 2022.