A kasar Germany, kimanin shekaru talatin da daya 31, da suka wuce, akayi wata shari’a akan wani mutun da ya dauki alhakin kashe wata mata. Yau bayan shekaru talatin da daya 31, sai ga matar ta bayyana cikin koshin lafiya a wani gari da ake kira Dusseldorf.
A shekarar 1984, Petra Pazsitka, mai shekaru ashirin da hudu 24, a wancan lokacin, ta bace a wani gari mai suna Braunscwigh, na yankin arewacin Germany, lokacin ta na zaune a gidan dalibai. Ta bayyanar da cewar ita ta shirya bacewar ta a wancan lokacin,
Yanzu haka dai matar ‘yar shekaru hamsin da biyar 55, tana amfani da wani suna Mrs. Schneider, jami’an ‘yan-sanda sun gano ta ne a lokacin da suke gudanar da wani bincike, a wani gida da akayi sata ciki. Matar dai ta bayyana ma ‘yan-sanda cewar, sunan dake rubuce a kofar gidan ba nata bane, domin kuwa itace matar da ta bace shekaru da suka gabata, kuma ta bayyanar da wani kati wanda yake dauke da sunanta na asali.
An tambayi Petra, dalilin ta na boye kanta tsawon wadannan shekarun, amma bata bada wani dalili mai gwari ba, domin kuwa rahoto ya nuna cewar tayi tsawon rayuwar ta, batare da tana da katin zama ‘yar kasa ba, ko kuwa katin izinin tukin mota. A karshe dai an umurce ta, da ta gabatar da kanta ga hukumomi don a sakata cikin jerin sunayen ‘yan kasa.