Amurka tace da akwai alamun "babbar dama" ta fuskar difilomasiyya na gudanar da shawarwari a taron MDD da za'a fara gobe litinin, da zai kai ga kawo karshen zubar da jini da ake yin a Yemen da kuma Syria, da kuma samun ci gaba na samun zaman lafiya a can.
Sakataren harkokin wajen Amurka John kerry ne yake bada haske da kwarin guiwa kan haka, bayan shawarwari da ya gudanar da takwaran aikins a na Iran Mohammed Javad Zariff, gabannin fara muhawara a zaman babban zauren Majalisar Dinkin Duniya na bana.
Mr. Kerry yace ya hakikance cewa akwai dama "na samun ci gaba" cikin kwanaki masu zuwa, lokacin da za'a gudanar da wasu shawarwari a gefen zaman Majalisar Dinkin Duniya.
Da yake magana, Zarif yace burinsa shine maida hankali kan aiwatar da yarjejeniyar da kasa da kasa ta kulla da kasarsa kan shirin Nukiliyarta ciki har da Amurka.
Ahalinda ake ciki kuma fiyeda kasashen duniya 200 ne suka sanya hanu kan sabon shirin muradun karni na bunkasa shirin yakar talauci, da jahilci, da koma bayan mata da sauransu. Wannan shine taron koli da aka fara ranar Jumma'a, inda shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da shugabannin wasu kasashe suka gabatar da jawabai.
Ga rahoto
Your browser doesn’t support HTML5