Iska Ya Jawo Cikas Ga Jirgin Saman Da Yafi Girma a Duniya

France Paris Air Show

Matuka jirgin sama na kamuwa da ciwon zuciya, ko kuma ace suna shiga mawuyacin hali, a wajen dai-dai ta saukar jirgi. Jiya ne jirgin sama da yafi kowan ne girma a duniya wato “Airbus A380” a turance, ya fuskanci kalubale mafigirma.

A yayin da jirgin ya bukaci sauka a tashar jirage na Dusseldorf a kasar Jamus, ya fuskanci wata iska mai muguwar karfi, wadda ta nemi kwashe kafafuwan jirgin.

A cewar wani wanda yayi kokarin daukar hoton jirgin, a lokacin da yake kokawar sauka, “Yace kimanin shekaru biyar da suka wuce, yaga yadda iska ke yiwa jirgi idan yazo sauka.

Amma bai taba ganin irin wannan ba, domin kuwa abun sai wanda ya gani.” Sai ya kara da cewar “Duk fika-fikan jirgin sun fito dai-dai, ga ban sha’awa, amma ganin jirgin da yafi girma na kokawa da iska, wannan wani abun mamaki ne.”

Abun jima a nan shine, baya ga karfin iskar sannan kuma titin jirgin na jike da ruwan sama. Shi dai jirgin mai hawa biyu na dauke da fasinjoji 853. Kuma yana da tsawon murbba’in 236, kana yakan dauki nauyin kaya da suka kai, pound milliyan daya da dugo ashirin da bakwai 1.27. Kuma yana da karfin tafiya daga jihohi masu nisa daga juna a kasar Amurka, kuma ya tafi kasar Sydney, ya kuma wuce kasar Australia, ba tare da ya tsaya ba.